<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>172</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Ubangiji ya ce, ku zo gare ni duk
 Da kayan laifinku, zan ba ku hutawa.

[V2]
 KORUS
 Shi ya biya duk domin laifina.
 Yesu ya hutad da ni, ya ba ni sabon rai.

[V3]
 2) Yesu, na gaskata ikonka, shi kaɗai,
 Zai sāke zuciyata, ya ba ni sabon rai.
 Korus

[V4]
 3) Ko kyau ba ni da shi, ban isa kome ba,
 Amma jinin Yesu ya wanke zuciyata.
 Korus</lyrics>
<title>Ubangiji Ya Ce, Ku Zo Gare Ni Duk LW172</title>
</song>